エピソードの概要
A cikin shirin namu na yau, za mu ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da dukkan matakan da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a zaɓen 2027. Za mu ji martanin Nafiu Bala Gombe, wanda ya shigar da ƙarar, da kuma martanin tawagar Atiku.
A cikin shirin namu na yau, za mu ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da dukkan matakan da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a zaɓen 2027. Za mu ji martanin Nafiu Bala Gombe, wanda ya shigar da ƙarar, da kuma martanin tawagar Atiku.
エピソード
Ɗaukaka ƙara daga ADC za ta dakatar da hukuncin kotu kan Atiku da jam'iyyar?
再生済みA cikin shirin namu na yau, za mu ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da dukkan matakan da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a zaɓen 2027. Za mu ji martanin Nafiu Bala Gombe, wanda ya shigar da ƙarar, da kuma martanin tawagar Atiku.
ADC ta magantu kan ikirarin da APC ta yi cewa Tinubu ya nada goyan bayan Arewa
再生済みA cikin shirinmu na yau tare da Michael Kuduson za mu yi waiwaye akan babban gangamin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a Kaduna,, inda shugabannin jam’iyyar suka yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da goyon bayan Arewa. Za mu kuma ji martanin jam’iyyar ADC kan wannan ikirari, musamman batun cewa sama da mutum miliyan ɗaya ne suka halarci gangamin. Latsa alamar sauti don sauraron karin bayani.....
Ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin INEC da saɓawa dokar zaɓe
再生済みShirin Dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya yi duba kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin cewa Hukumar Zaɓen Najeriye, ta gaza wallafa rajistar masu zaɓe a intanet cikin wa’adin da dokar Zaɓe ta tanada. Sai dai hukumar ta ce ba ta karya doka ba. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Jami'iyyar APC ta kaddamar da majalisar yaƙin neman ta a hukumance
再生済みShirin dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali kan ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, da kuma martani akan zaɓen zaɓi jihar Kaduna a matsayin wurin fara gangamin Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Shirin ragin kuɗin man fetur na wata 1 ya janyo cece-kuce a Najeriya
再生済みShirin ‘Dandalin Siyasa’ tare da Michael Kuduson a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya kan shirin samar da rangwamen farashin man fetur na tsawon kwanaki 30, da martanin ’yan adawa. Sannan za mu waiwayi hukuncin Kotun Ƙoli da kuma matsayin Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, kan jam’iyyun siyasar da suka saɓa ƙa’idojin miƙa rajistar mambobinsu, da dai sauran batutuwan da muka tanadar muku a shirin. A daidai lokacin da ƴan Najeriya ke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, musamman farashin man fetur da sufuri, gwamnatin ƙasar ta sanar da wani mataki na rage nauyin da ke kan al’umma. Gwamnatin ta ce za a sayar da man fetur bisa rangwame a gidajen mai na kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC, na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu jigilar fasinjoji fifiko. Sai dai mataki bai burge ƴan adawa ba, domin kuwa sun mayar da martani, inda suke ke tambaya ko rangwamen na ɗan lokaci zai iya magance matsalolin da suka shafi tsadar rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakke shirin.